Shafin Farko

Burawuza


Gabatarwa

Burawuza, wacce ake kira browser a Turance, suna ne na softuwaya wadda ka iya zama ta kwamfuta ko kuma ta wayar hannu wadda ake amfani da ita wajen buɗe shafukan Intanet. Wato ita ce take buɗe wa mai amfani da kwamfuta ko waya duk wani shafin Intanet.

Akwai Burawuzozi da dama da ake amfani da su a kwamfuta da kuma waya. Daga cikin su akwai Gugul Kurom (Google Chrome), Ofera-Mini (Opera Mini), Mozilla Fayafoks (Mozilla Firefox) da sauransu. Waɗannan uku da na kawo, su aka fi yawan amfani da su a waya da kuma kwamfuta. Wato dukkansu akwai wadda ake amfani da ita a kwamfuta domin buɗe shafukan Intane sannan kuma akwai ta wayar hannu.

Babban amfanin burawuza shi ne buɗe dukkanin shafukan Intanet tare kuma da bayar da damammakin adana shafi, yaɗa shafi (Tura shafin zuwa ga wani), fitar da rubutu a kan takarda da sauran abubuwa. Shafuka irin su www.rumbunilimi.com.ng,www.maidarasu.com.ng, www.bbchausa.com,www.ɓoahausa.com da sauransu duk da burawuza ake buɗe su. Latsa nan domin ganin yadda ake buɗe shafukan Intanet da burawuzar waya.

Manazarta:


Tsangarwa A.M. (2010). Kwamfuta a Sauƙaƙe, Sabon Bugu. Tsangarwa ICT Limited, Kano-Nigeria.